Monday, September 11, 2017

HUKUNCIN SHARI’A BASHI TABBATUWA SAI DA DALILI INGATACCE KUMA BAYYANANNE

Hukunce-hukunce na shari’a guda biyar ne: Wajibi, da Haramun, da Mustahabbi, da Makruhi, da Mubahi. Babu mai ikon ya tabbatar da daya daga cikinsu sai shari’a, kamar yadda bai halatta a yi da’awar daya daga cikinsu ba sai da dalili.

WAJIBI shine duk wani abu da shari’a ta yi umarnin yinsa yanke, kuma wanda ya aikata yana da lada, wanda ya ki aikatawa kuma ya yi laifi.

HARAMUN shine duk wani abu da shari’a ta yi hani a kansa yanke, kuma duk wanda ya aikata yana da alhaki, wanda ya ki aikatawa kuma yana da lada.

MUSTAHABBI shine duk wani abu da shari’a ta kwadaitar bisa aikata shi. Mai aikata shi yana da lada, amma ba shi da laifi don bai aikata ba.

MAKRUHI shine duk wani abu da shari’a ta ki shi, ba tare da mai aikata shi ya zamo mai laifi ba.

MUBAHI shine duk wani abu da shari’a ta bayar da izinin za’a iya aikatawa ko a bari.
To dukkan wadannan suna tabbata ne daga Allah da Manzonsa.
Dalilin wannan ka’idar shine fadin Allah Madaukaki:

ولا تقولوا لما تصف ألستنكم الكذب هذا
حلال وهذا حرام لتفتروا على الله الكذب إن الذين يفترون على الله الكذب لا يفلحون

“Kuma kada ku fadi abin da harsunanku suke siffatawa na karya cewa, wannan halal ne wannan kuma haram ne, don ku yi wa Allah karya. Hakika wadanda suke kira wa Allah karya ba su rabauta”. Nahl: 116

Da fadinsa:
ولا تقف ما ليس لك به علم إن السمع والبصر والفؤاد كل أولئك كان عنه مسؤولا

“Kada kuma ka dinga bibiyar abin da ba ka da ilimi a kansa. Hakika ji da gani da kuma tunani duk wadannan sun zama abin tambaya game da su”. Isra’: 36

Hankali ba zai iya kadaituwa wajen riskar shari’a dalla-dalla ba, shi ya sanya mutane suka bukatu izuwa aiko manzonni da kuma saukar da littattafai, don shiryar dasu zuwa hanyar bautawa Allah. Da a ce hankula zasu iya kadaituwa da hakan, da ba’a bukaci aiko Manzonni da sakko da littattafai ba.

Saboda haka: Duk wani abu da ya danganci ibada, na tabbatar da ita asalinta, ko wata siffa, ko lokaci, ko bigire, ko sharadi, ko sababi, dukkan wadannan suna cikin dangogin hukunce-hukunce na shari’a, kuma dole kafin a tabbatar da su a kawo dalilin hakan, dalilin kuma ya zamo ingatacce kuma bayyananne, duk abin da dalili ya tabbatar shine yake zamowa ibada ta gaskiya, wanda bai tabbatar ba kuma ba shi samun mazauni cikin shari’a.

Wassalamu Alaikum.

No comments:

Post a Comment

BE GRATEFUL TO YOUR PARENTS

His mother carried him in difficulty, hardship and danger which could result in her death. Thereafter, she educates and nurtures you and spe...