Sunday, September 24, 2017

SAQON MARABA DA SABUWAR SHEKARAR, 1439 HIJRAH

Wannan rubutu ne daga babban malamin mu Shekh Muhammad Bn Uthman Kano limamin masallacin Sahaba kundila.

Wanda yayi acikin wasu shafukan takardu Guda 2 a shekarar 1439H, 2008 in da naga ya dace in dakko shi in masa gyara in canja inda akayi bayani da lafazin waccan shekarar in kuma rubuta shi dan al'umma su amfana da abin da wannan rubutu ya fadakar dan haka sai mai karatu ya biyomu dan fa'idan tuwa.

Godiya ta tabbata ga Allah sarkin baiwa, mai kowa mai kome, tsira da amincin su kara tabbata ga shugabanmu, Annabi Muhammad, mai gaskiya abin gaskatawa, tare da iyalan gidan tsarkaka da kuma sahabbansa nagartattu, da kuma duk wanda ya bisu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

Bayan haka wadannan bayanai'yan kadan, suna magana ne kan matashiyar da ta gabata:-

*"MARABA DA SABUWAR SHEKARAR MUSULUNCI TA 1439"*

Wannan Maraba kuwa ta kunshi sakonni ne Guda 10, nake mikawa ga 'yan uwa musulmi, maza da mata. Allah ta'ala ya amfanar Damu dasu ganba daya da wannan sakonni, lallai shi ne maijibintar haka, kuma mai iko akai.

                           *Ga sakonnin:-*

1- Ba dai dai bane garemu al'ummar musulmi, ace muna da wayewa da fahimta kan sabuwar shekarar bature ta kiristanci wato shekarar kalandar fafaroma girigori (pope gregorey) amma fahimtar da yawa cikin mu kan ta musulunci yar kadance ko babu ma dungurungun!

Mutuna fa: "Na Allah shi yake tabbata, Amma dukkan wanda banashi ba mai gushewa ne"
Kuma"Naka shi ne naka".

2- Asalin bukuwan shigowar sabuwar shekarar bature, bukukuwa ne da suke da nasaba da bautar gumaka da shirka.

Misali Gunkin Janus (January) me ya hada musulmi da kunna kyandira a daren fadowar shekara?!

Me yakai musulmi mabiyin Manzon Allah (S.A.W) shiga sharo ba shanu?

Har kaga yana aikawa da katin gaisuwar sabuwar shekara. Shin wannan taimakawa kiristanci ne ko ko a'a?, mu tuna fa cewa:-" Wanda ya daka rawar wani......... "

3- Dan Allah 'yan uwa masu girma me yasa muka fi haddace sunayen watanin boko tun daga janairu (January) zuwa disamba (December)?

Amma mafiya yawan mu da kyar in zasu iya kawo maka watannin musulunci a jere. Menene dalili?! Aikin gwamnati?, Tsabagen rashin baiwa karatun Addini muhimmaci ne? Mutuna Annabin mu (S.A.W) yace: "Wanda Allah yake nufin sa da alkairi sai ya fahimtar dashi addini". Ruwayar bukhari.

4- Dan Allah ina so ka ba ko ki ba kanka/kanki amsa kan wannan tambayar:-

Shin rashin, ko in ce karancin amfani da kididdigar kalandar musulunci a al'amura da dama kamar Aure, mutuwa, haihuwa da sauran su, maimakon haka munfi yin amfani da ta bature shin ci gaba da yin hakan kara dakile kokarin wayar da kan musulmi ne kan TSARIN rayuwa irin na musulunci ko kuwa a'a?!.

5- Ya kamata kai! Ya ma wajaba mu kara sanin cewa ita fa wannan kalanda ta musulunci an dorata ne kaco kan a kan hijirar Annabi Muhammad(S.A.W) ita kuma hijra itace harsashen daukakar musulunci.

Menene harsashen kalandar musulunci?
Amsa: Hijra.

Menene harsashen kalandar bature?
Amsa: Maguzanci. Ashe ruwa basa'an kwando bane!.

6- Ya kamata mu waiwayi shekarar bays wadda ta wuce 1438H. Mu waiwayeta, muna masu nadama kan abubuwanda muka aikata Wanda ba dai dai ba mu tuba,mu gyara.

Domin shekarar dai ta tafi ta tafi da dukkanin bayanan abubuwan da muka aikata in al'kairi al'kairi, in sharri, sharri,- INNA LILLAHI WA INNA ILAY'HI RAAJI'UUN- Mu kuma dai waiwayeta muna la'akari da abubuwan da muka aikata Na kirki domin mu kara zage damtse akan cigaba da su a wannan shekara 1439.

wannan shi ake kira YI WA KAI HISABI magabata sun kasance sunacewa:- "KUYI WA KANKU HISABI KAFIN AYI MUKU HISABI".

7- Mu yiwa kokarin mu haddace sunayen watannin nan tare da sanin ma'anonin su, mu kuma koyawa yara musamman ma dai a wake domin saukin haddacewa.

8- Mu yiwa kawunanmu jadawalin ayyuka Na shekara (New year Planner).

Misali:- A wannan shekarar tamu ta musulinci,1439, Na tsarawa kaina kafin karewar ta insha Allah:-

a. Zan kammala haddar Qur'ani.
b. Sauke Qur'ani sauka kaza.
c. Ciyar da marayu guda kaza.
d. Agazawa mata wadanda aka mutu aka bar musu marayu guda kaza.
e. Dauke nauyin masu fita da'awa (Islamic Propagation) su mutum kaza.
f. Daukar nauyin buga littafai da kuma yan takardu masu dauke da sakonnin musulunci bisa karantarwar sunnar Manson Allah (S.A.W).
g. Daukar nauyin gyara sifikoki Na masallatai guda kaza.

Da dai sauran ayyuka Na al'kairi masu yawa Allah ya bamu dacewa.

9- Babu wani dalili ingantacce kan shirya wash bukukuwa da sunan murnar sabuwar shekara.

10- Kada mu manta da yin azumi ranar Tara da kuma goma (Tasuu'a da Aashuura) a wannan wata da zai kama.

Dan gane da Ashuura A'limamu Muslim ya fitar da hadisi daga Abu Qataada (R.A) cewa Manson Allah (S.A.W) yace:- *"Azumin ranar ashuura Na kankare zunuban shekara wadda ta shude"* Amma dangane da ranar Tasu'a kuwa akwai hadisi cikin musnad Na imamu Ahmad da isnadi "jayyid" cewa Manzon Allah (S.A.W) yace:- *"in har Na rayu zuwa shekara Mai zuwa,zan azumci Tara (wato tasuu'a)"
Allah cikin ikonsa Manson Allah (S.A.W) bai yi ba zuwa wannan shekara ta gaba.

Dan haka kenan shi azumin ashuura nassi ne tare da aikin Manson Allah (S.A.W).

Amma shi Na Taasuu'a kuwa isharar da yayi -S.A.W- ita ta Bada hukunci mai karfi kan yin wannan azumi, wannan shi ne irin matsayin da al'imamush Shafi'y R.L da sauran malamai suke dashi.

Allah ya bamu alkairan dake cikin wannan wata da kuma shekarar, sharrin da ke ciki Allah ya tsare mu daga gare shi. Amin summa Amin.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.

No comments:

Post a Comment

BE GRATEFUL TO YOUR PARENTS

His mother carried him in difficulty, hardship and danger which could result in her death. Thereafter, she educates and nurtures you and spe...